(ABNA24.com) Gwamnatin Siriya, ta yi watsi da rahoton hukumar yana yaduwar makamai masu guba ta duniya (OPCW), wanda ke cewa sojojin kasar ne ke da hannu a amfani da makamai masu guba a arewacin kasar a cikin shekara 2017.
Kamfanin dilancin labaren Siriya na (Sana), ya rawaito cewa, wannan rahoton na OPCW, ba shi da tushe balle makama.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Siriya ta fitar, ta ce sakamakon rahoton marar tushe, an kirkiro ne domin domin kawai zargin gwamnatin Siriya da kai harin.
Siriya ta ce tana mai watsi da gabadayan rahoton da kuma kara nanata cewa babu hannunta a kai harin na makamai masu guba a arewacin kasar.
A ranar Laraba ne, hukumar hana yaduwar makamai masu guba ta duniya, OPCW, ta fitar da rahoton da ta ce, sojojin gwamnatin Bashar Al-Assad, ne suka kai harin da makami mai guba samfarin iskar gas na‘’chlore’’ a yankin Latamne dake arewacin kasar a shekara 2017.
Kuma wannan shi ne karon farko da hukumar ta OPCW dake da cibiya a La Haye, ta zargi gwamnatin Siriya da kai hari makamancin wannan a cikin kasarta.
/129